Mr. Malki ya ce, ba za'a amince ko kuma yarda da matakin Benjamin Netanyahu ba, firaministan gwamantin Isra'Ila ya saci moriyar al'ummar Palesdinu ya kara saurin gina matsugunan Yahudawa domin cimma burinsa na samun nasara a yakin takara tsakanin jam'iyyun siyasar Isra'ila ba.
Mr. Malki ya kara da cewa, yanzu bangaren Palesdinu na jira bangaren Amurka ta dakatar da shirin Netanyahu. Idan ba zai yi hakan ba, bangaren Palesdinu zai dauki matakai nasa ga ayyukan gina matsugunan Yahudawa da ake hanzarta ginawa.
Yanzu gwamnatin Isra'ila tana son amincewa da shirin gina karin gidaje 3829 ga Yahudawa a wasu yankunan dake yammacin kogin Jordan. An yi hasashen cewa, za a amince da shirin a yayin taron babban kwamitin tsara shirye-shirye na hukumar kula da harkokin al'umma ta Isra'ila da za a shirya a ran 16 ga watan nan. (Sanusi Chen)