in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nanana matsayinta na samar da 'yantacciyar kasar Palesdinu
2018-01-26 10:04:21 cri
Wakilin kasar Sin a MDD ya nanata matsayin kasar Sin na samar da 'yantacciyar kasar Palasdinu a matsayin babbar hanyar da zata kawo karshen zaman tankiya a rikicin gabas ta tsakiya.

Da yake jawabi a taron mahawara na kwamitin sulhun MDDr game da batun matsalar Palasdinawa, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana cewa, kawo karshen matsalar al'ummar Palstinawa ita ce kadai mafita wajen samar da dauwamamman zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, ya ce samar da kasashen biyu masu ikon cin gashin kai ita ce babbar hanyar da al'ummar kasa da kasa za su himmatu da kuma kudurorin MDD game da wanna batu, da shirin wanzar da zaman lafiya.

Kasar Sin tana goyon bayan baiwa al'ummar Palasdinawa kasarsu mai cikakken 'yancin gashin kai, kuma a maido musu cikakken ikon mallakar kasarsu bisa tsarin dokar shata kan iyakoki ta shekarar 1967, wanda ya amince da gabashin kudus a matsayin babban birnin Palasdinu, inji wakilin na Sin.

Ya ce wannan matsayi ba zai taba sauyawa ba, inda ya bayyana matsayin kasar Sin na gabatar da kudurori hudu wadanda dukkansu sun kunshi yin kiraye-kiraye na neman amfani da matakin siyasa wajen warware takun sakar dake tsakanin bangarorin biyu, inda yace hakan zai tabbatar da samun cikakken tsaro, bisa ga kokarin kasa da kasa, kuma matakin zai kawo dauwamamman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China