in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Palesdinu ya yi tir da kasar Amurka game da haramta samar da kudin gudummawa ga Palesdinu
2018-01-20 13:31:26 cri
Jami'in kungiyar 'yantar da Palesdinu wato PLO mai kula da harkokin 'yan gudun hijira Zakaria al-Agha, ya yi tir da kasar Amurka game da haramta samar da kudin tallafin samar da abinci ga 'yan gudun hijirar Palastinawa da yawan kudin ya kai dala miliyan 45.

Al-Agha ya bayyanawa 'yan jarida a wannan rana cewa, Palesdinu ta yi tir da matsayin kasar Amurka a wannan fanni domin wannan ne kashin farko daga cikin yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da kasar Amurka ta gabatar. Ya bayyana cewa, kasar Amurka ta yi wannan aikin don rufe ofishin MDD na samar da gudummawa ga Palasdinawa 'yan gudun hijira da raya ayyuka a yankin Near East wato UNRWA don biyan basussukan da ofishin yake bi, da kuma yin hukunci ga jama'ar Palesdinu.

Wannan ne karo na biyu da kasar Amurka ta tabbatar da haramta samar da kudin gudummawa ga Palesdinu a wannan mako. A ranar 16 ga wannan wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar da haramtar samar da kudin gudummawa da yawansu ya kai dala miliyan 65 ga 'yan gudun hijira na Palesdinu ta hanyar ofishin UNRWA, kana ta bukaci ofishin ya yi kwaskwarima.

An kafa ofishin UNRWA ne a shekarar 1949, wanda ke kula da aikin samar da gudummawar jin kai da bada ilmi da kiwon lafiya da sauransu ga Palestinawa 'yan gudun hijira da yawansu ya zarta miliyan 5 da suke rayuwa a yankunan yammacin gabar kogin Jordan, zirin Gaza da kasashen Jordan, Syria da Lebanon. Kasar Amurka kwa ita ce muhimmin bangare na samar da kudi ga ofishin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China