Simon wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin a Mogadishu, yayin da yake jawabi yayin cin abincin rana a taron tuntubar juna na kwanaki 4 da kungiyar IGAD ta shirya game da yadda za a saukaka zirga-zirga tsakanin al'ummomin nahiyar ya ce, kungiyar tana hada kai da hukumomin tattalin arziki da ragowar masu ruwa da tsaki dake yankin don fito da matakan da za su tabbatar da ganin an cimma wannan buri.
Mulongo ya yi maraba da matakin na IGAD, yana mai cewa, zai taimaka wajen bunkasa harkokin cinikayya da hade tattalin arzikin yankin waje guda
Yanzu haka dai, kungiyar mai mambobi 8 tana kokarin saukaka zirga-zirga tsakanin al'ummomin kasashen nahiyar ta yadda za su rika yin cinikayya a yankin da ya kai fadin murabba'in kilomita miliyan 5.2 ba tare da wani shinge ba.(Ibrahim)