in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sassou-Nguesso: labarin "leken asirin kungiyar AU" jita-jita ce
2018-02-10 12:57:53 cri
Denis Sassou-Nguesso, shugaban kasar Jamhuriyar Congo, ya yi hira da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua a kwanakin baya, inda ya ce, wani labarin da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka gabatar a yayin jerin tarukan karkashin laimar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU karo na 30, wai "kasar Sin ta yi leken asirin kungiyar AU" jita-jita ce da ba ta da tushe ko kadan. Maimakon nuna imani kan wannan jita-jitar da aka yada, kasashen Afirka sun nuna yabo ga kasar Sin bisa manufar da ta dauka ta kokarin tallafawa nahiyar Afirka. A cewar shugaban kasar Congo, daukacin kasashen dake nahiyar Afirka za su ci gaba da amfanawa da matakan da kasar Sin ta dauka.

Dangane da batun tallafawa kasashen Afirka gina babban ginin hedkwatar kungiyar AU a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, da kasar Sin ta yi, shugaba Sassou-Nguesso ya ce, dukkan sassan nahiyar Afirka suna maraba da tallafin da kasar Sin ta bayar. Wannan babban ginin da aka fara yin amfani da shi yanzu wata shaida ce ga zumunci mai zurfi dake tsakanin jama'ar kasar Sin da al'ummar kasashen Afirka, wadda ta janyo yabo da yawa daga kasashen dake nahiyar Afirka daban daban.

Shugaban ya kara da cewa, ya kamata a gaya ma wadannan kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya, wadanda suka yada jita-jitar a wannan karo, cewa a hakika dukkan ayyukan da shugabannin kasashen Afirka suka gudanar a cikin babban ginin hedkwatar kungiyar AU a bayyane suke, babu sirri a ciki. Ban da haka kuma, dukkan kayayyaki da na'urorin da ake amfani da su cikin ginin, an shigo da su ne daga kasashe daban daban, bisa matakin neman tanda. Saboda haka, zancen da aka yi, wai kasar Sin ta ajiye wasu na'urorin daukar muryar asiri cikin ginin hedkwatar kungiyar AU, ba maganar gaskiya ba ce.

Haka zalika, shugaban kasar Congo ya kara da cewa, a zamanin da muke ciki, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da Sin ta riga ta zama wani abin koyi ga daukacin kasashe masu tasowa, wadanda su ma suke da bukatar gudanar da hadin kai tsakanin junansu. Sa'an nan, a watan Satumban bana, za a bude wani muhimmin biki, wato taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin. Kafin kaddamarwar taron, kasashen Afirka na tare da burin ganin kasar Sin ta kara taimaka musu, a kokarinsu na sauya fasalin tattalin arziki, da neman dauwamamen ci gaban al'umma.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China