WHO ta kara da cewa, la'akari da lalacewar hanyoyin ruwa da kayayyakin tsaftace muhalli, mazauna yankunan da iftila'in ya shafa a kasar dake yammacin Afrika na cikin hadarin fuskantar barkewar wasu cututtukan da da ma akwai su a kasar, wadanda suka hada da zazzabin cizon sauro da cututtukan da kan haifar da amai da gudawa da suka hada da zazzabin gudanawa da kwalara.
Barkewar cutar kwalara da aka samu a kasar a baya-bayan nan ya auku ne a shekarar 2012.
A yanzu haka, WHO na aiki da hukumomin lafiya dake kasar domin kara kaimi wajen daukar matakan kariya da kuma tunkarar barkewar cututtuka. (Fa'iza Mustapha)