in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar likitoci ta dakarun kasar Sin ta duba lafiyar sama da mutane 70 da ibtila'in Saliyo ya shafa
2017-08-21 13:37:45 cri

Tawagar likitoci masu aikin jin kai na rundunar sojin 'yantar da al'umma ta kasar Sin (PLA) dake kasar Saliyo, ta duba lafiyar sama da mutane 70 wadanda ibtila'in zaftarewar laka na ranar 14 ga watan Agusta ya shafa a Freetown babban birnin kasar ta yammacin Afrika. Guo Xuejun, shi ne shugaban tawagar ya bayyana cewa, tagawar tana gudanar da aikin ba da agaji game da rage radadin bala'in ta hanyar yin hadin gwiwa da rundunar sojin kasar Saliyo wajen kafa sashen duba lafiyar mutanen da suka samu raunuka a sanadiyyar abkuwar ibtila'in.

Ya ce kasar Saliyo tana fama da matsalolin cutuka masu saurin yaduwa, kuma akwai matsaloli na yaduwar cutar zazzabin cizon sauro, da wasu cutukan da suka shafi kayan cikin dan adam da ke addabar jama'a a kasar.

Guo ya ce, halin da jama'ar suka tsinci kansu na yawan cunkoso sakamakon sauya musu matsugunai sakamakon faruwar ibtila'in da kuma karuwar yanayin zafi da ake samu, zai iya haifar da barazanar barkewar cutuka, wanda hakan wata babban bala'i ne.

Ya ce domin hana fadawa cikin wannan yanayi, tawagar kula da lafiyar ta tsabtace wuraren zaman, inda ta yi feshin magungunan kashe kwari, don hana yaduwar kwayoyin cutuka. Tagawar kwararrun likitocin sun samar da kayayyakin kula da lafiya ga mutanen da bala'in ya shafa, inda za su koya musu yadda za su yiwa kansu rigakafin kamuwa daga cutukan.

A cewar Guo, tagawar lokitocin rundunar sojojin ta yi nazarin game da yiwuwar barkewar cutukan, kuma ta bayar da shawarwari game da matakan da za'a dauka don samar da kariya daga kamuwa daga cutukan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China