in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi ta'aziyya ga kasashe mambobinta bisa rasa rayuka da aka samu sanadiyyar tsagewar kasa da zaftarewar laka
2017-08-24 10:08:10 cri
Wakiliyar shugaban kungiyar tarayyar Afrika AU ta isa kasar Saliyo domin duba irin barnar da zaftarewar laka ta haddasa a ranar 15 ga watan Augasta a kasar, kana da mika kayayyakin tallafi.

Sanarwar da AU ta fitar tace, shugabar sashen walwalar jama'a ta kungiyar Amira Elfadil, ta isa birnin Freetown ne tun a ranar Talata, domin bayyana goyon bayan AU da kuma tallafawa gwamnatin Saliyo sakamakon ibtila'in da ya afku.

AU zata mika cakin kudi na dalar Amurka dubu 100 a matsayin wani bangare na gudumowar da AU ta baiwa gwamnatin Saliyo, sakamakon ibtila'in zaftarewar laka, wanda yayi sanadiyyar hallaka akalla mutane 500, kana wasu sama da 600 suka bace, sannan wasu dubban mutane suka rasa matsugunansu.

Bugu da kari, a wata sanarwar ta daban, shugaban na AU ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnatin Guinea da ta jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC, sakamakon bala'in tsagewar kasa da aka samu a kasashen wanda ruwan sama ya haddasa.

A kalla mutane 8 ne suka hallaka a gundumar Ratoma dake wajen birnin Conakry hedkwatar mulkin kasar Guinean, yayin da mutane 200 kuma suka rasa rayukansu a lardin Ituri dake arewa maso gabashin DRC.

Shugaban kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya jaddada aniyar AU wajen tallafawa kasashen nahiyar Afrika don daukar kwararan matakai na tunkarar afkuwar bala'o'i.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China