in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da ayyuka 19 da za a gudanarwa bisa shirin AREI
2017-03-06 15:06:10 cri
Kwanan baya, ministar kula da harkokin muhalli, makamashi da teku ta kasar Faransa madam Ségolène Royal ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu an riga an tabbatar da ayyuka guda 19, wadanda za a gudana bisa shirin sarrafa makamashi irin na bola jari a Afirka ko AREI a takaice.

An kaddamar da wannan shiri ne a watan Disamban shekarar 2015 a birnin Paris na kasar Faransa, bisa yarjejeniyar Paris, wadda masu sa hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayin MDD suka cimma.

Burin shawarar shi ne, ya zuwa 2020, kasashe da yankuna masu ci gaba, da hukumomin kudi na duniya za su samar da dallar Amurka biliyan 10 ga Afirka, don taimaka wa nahiyar raya aikin makamashi na bola jari. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China