in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen Afirka na fadada hadin gwiwa a fannin makamashi da ake iya sabuntawa
2017-08-31 19:35:12 cri
Yanzu haka kasar Sin da takwarorin ta na nahiyar Afirka, na kara kaimi wajen fadada hadin gwiwarsu a fannin samar da makamashi da ake iya sabuntawa.

Hakan dai na zuwa a gabar da kasashe masu tasowa, ke dada bunkasa shirin su na inganta amfani da wadannan nau'o'i na makamashi, da kuma kare muhalli daga gurbata.

Yanzu haka dai kungiyar hadin gwiwar Sin da Afirka kan bunkasa makamashin da ake iya sabuntawa da kirkire kirkire, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, wadda za ta share fagen hadin gwiwa da cibiyar bunkasa makamashi mai tsafta ta Afirka ko AREI a takaice.

Yarjejeniyar da aka sanyawa hannu a jiya Alhamis dai na da nufin baiwa sassan biyu, damar bunkasa samar da makamashi da ake iya sabunta amfanin shi, ta yadda kamfanonin Sin za su samar da dukkanin kudade da kwarewar da ake bukata, domin cimma nasarar kara yawan wadannan nau'o'i na makamashi da ake bukata a nahiyar ta Afirka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China