in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DA ta lashi takobin haramta yarjejeniyar da ta shafi makamashin nukiliya
2017-11-06 10:25:44 cri

Jam'iyyar adawa ta kasar Afrika ta kudu Democratic Alliance DA, ta lashi takobin haramta duk wani yunkurin gwamnatin kasar na cimma yarjejeniya game da makamshin nukiliya.

Wannan na zuwa ne bayan jaridar City Press ta ruwaito a jiya Lahadi cewa, ministan makamashin kasar David Mahlobo ya fara amfani da shirinsa na makamashin nukiliya, inda jami'an ma'aikatarsa ke aiki a karshen mako domin kammala sake fasalin tsarin makamashin kasar cikin nan da makonni biyu, watanni 4 kafin lokacin da aka tsara.

A cewar ministan makamashi na jam'iyyar adawa Gardon Mackay, a bayyane yake cewa, an nada David Mahlobo ne domin tabbatar da cimma yarjejeniyar makamashin nukiliya.

Ya ce, shugaban kasar Jacob Zuma ya nada David Mahlobo a matsayin minista watan da ya gabata ne a wani yunkurin da ake ganin na da nufin gaggauta cimma yarjejeniyar makamashin nukiliya da Rasha.

Gardon Mackay ya kara da cewa, ba za su kyale Mahlobo ya farantawa abokansa Rashawa ta hanyar batawa miliyoyin al'ummar kasar dake fafutukar rayuwa ba tare da aikin yi ba.

Ya ce, jam'iyyar DA za ta yi amfani da duk wani matakin shari'a da dokoki da take da su wajen tabbatar da ba a lalata makomar kasar ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China