in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin makamashi na Afirka zai tattauna batun makamashi mai tsafta
2017-11-10 12:51:12 cri

Yanzu haka an tabbata cewa, kasar Morocco ce za ta karbi bakuncin taron dandalin tattaunawa kan makamashin da ake iya sabuntawa na Afirka (ARF) wanda zai gudana daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamban wannan shekara a Casablanca, cibiyar kasuwancin kasar.

Taron wanda ake sa ran zai hallara ministocin makamashi na kasashen Afirka, da wakilan gwamnatoci, da manyan masu zuba jari, da masana da hukumomin kasa da kasa, zai tattauna batutuwan da suka shafi makamashi mai tsafta.

Bugu da kari, mahalarta taron za su yi musayar ra'ayoyi kan hanyoyin kara zuba jari a bangaren makamashi mai tsafta da kayayyakin more rayuwar jama'a ta yadda za a raya harkokin tattalin arziki maras gurbata muhalli da samun ci gaba mai dorewa a nahiyar.

Ana kuma sa ran mahalarta taron za su kara bullo ta matakan samar da kudaden tafiyar da ayyukan makamashi maras gurbata muhalli da magance matsalar sauyin yanayi da yadda al'ummomin za su rika kirkiro ayyukan da za su ci gajiyarsu.

Hukumar kula da makamashin da ake sabumtawa ta kasa da kasa na cewa, nan da shekarar 2030 makamashin da ake iya sabumta a Afirka zan ninka sau hudu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China