in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Kenya ya tattauna da shugaban 'yan adawa
2018-03-10 13:22:44 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya tattauna da shugaban 'yan adawa Raila Odinga jiya Jumma'a a Nairobi, babban birnin kasar, inda suka amince su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu.

Shugabannin biyu da suka yi jawabi ga wani taron manema labarai na hadin gwiwa, sun ce ganawar ta jiya ta bude wani sabon babi ga kasar.

Shugaba Kenyatta ya ce daga jiyan, shi da dan uwansa sun amince su fara shirin hada kan mutanensu.

Shugabannin sun kara da cewa, sun yanke shawarar aiki tare don samar da ci gaba da hadin kai a kasar dake gabashin Afrika, wadda ke fama da rarrabuwar kawuna saboda kabilanci, biyo bayan babban zaben watan Agustan bara.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce za su fara shirin hada kan al'ummarsu, tare da gano asalin abun da ya raba kan kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China