Kenyatta ya bayyana cewa, Sin da Kenya sun sada zumunta a dogon lokaci. A cikin shekaru fiye da 600 da suka gabata, kasashen biyu sun samu nasarori na hadin gwiwa. Ya ce ya yi imani da cewa, za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Kenya zuwa wani sabon matsayi a nan gaba.
Kenyatta ya bayyana cewa, Sin da Kenya sun yi hadin gwiwa wajen kafa hanyoyin jiragen kasa a tsakanin Mombasa da Nairobi da sauran manyan ayyuka, wadanda suke kyautata zaman rayuwar jama'ar Kenya. Shugaban ya ce hanyoyin jiragen kasa a tsakanin Mombasa da Nairobi aiki ne mafi girma na more rayuwa a gabashi da tsakiyar nahiyar Afirka, kana alama ce ta shaida hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin kasashen Sin da Kenya da jama'arsu. (Zainab)