in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta yi alkawarin inganta tsaron teku don bunkasa tattalin arziki daga albarkatun tekun
2018-03-01 09:59:30 cri
Hukumar tabbatar da tsaro ta kasar Kenya ta sha alwashin tabbatar da tsaron gabar tekunan kasar domin tabbatar da samun bunkasar tattalin arzikin da ake samu daga albarkatun cikin teku, a matsayin matakin da zai taimaka wajen samar da abinci ba tare da fuskantar barazanar tsaro daga masu fashin teku ba.

Raychelle Omamo, babbar sakatariyar hukumar tabbatar da tsaron kasar, ta ce, tabbatar da tsaron gabar tekun, wani muhimmin mataki ne da zai tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, a fannonin da suka hada da aikin gona, kamun kifi, sufuri da harkokin masana'antu.

Omamo ta ce, batun bunkasa tattalin arzikin da ake samu daga albarkatun cikin teku yana daya daga cikin muhimman ajandodi 4 na gwamnati mai ci, musamman wajen samar da abinci da fannin masana'antu. Ta kara da cewar hikimar dake tattare da inganta tattalin arzikin da ake samu daga albarkatun cikin teku zai taimaka wajen samar da dunbun arziki da kuma sabbin ayyukan dogaro da kai.

Ta bayyana hakan ne a lokacin taron tattaunawa da jami'an diplomasiyya na kasashen ketare dake Kenyan game da yadda za'a karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen waje a fannin tsaron teku da kuma albarkatun cikin teku.

Omamo ta ce, kasar Kenya ta bullo da wasu tsare-tsare da dokoki da za su taimaka wajen inganta sha'anin teku, da mahallin halittu da nufin tunkarar kalubaloli da suka shafi yunwa, da karancin abinci mai gina jiki, rashin aikin yi, da matsalar yaduwar cutuka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China