in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin kasar Sin zai bunkasa bangeren samar da gine-gine na kasar Kenya
2018-03-09 10:16:29 cri
Shugaban kamfanin gine-gine na Knight Frank dake kasar Kenya Ben Woodhams, ya ce jarin kasar Sin na bunkasa bangaren samar da gine gine ta hanyar amfani da fasahohi na zamani.

Ben Woodham ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan kwangilar kasar Sin suna kokarin yin aiki mai nagarta cikin lokaci kankani idan aka kwatanta da kamfanonin gine gine na kasar.

Ya ce 'yan kwangilar Sinawa, sun bullo da wani yanayi mai kyau na yin takara a fanin samar da gine gine, wanda ya ce ya yi kyakkyawan tasiri kan tattalin arziki ta hanyar rage farashin gidaje ga masu saye. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China