in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin shirye tafiye-tafiye a Kenya za su mai da hankali kan ziyarar kasuwanci a kasar Sin don kara kudaden shigarsu
2018-02-20 12:56:28 cri

Kamfanonin dake shirya tafiye tafiye a Kenya sun ce za su kara dora muhimmanci kan shirya yin tafiye-tafiyen kasuwanci zuwa kasar Sin don kara samun kudaden shigarsu.

Mohammed Wanyoike, shugaban kungiyar masu shirya tafiye tafiye na kasar Kenya (KATA), ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a Nairobi jiya Litinin cewa, jami'an su suna samar da kyakkyawan tsari ga masu sha'awar yin tafiye tafiye domin sayen kayayyakin a kasar Sin.

Ya ce, tafiye tafiyen kasuwanci zuwa kasar Sin yanzu ya kasance wani muhimmin batu wanda ke matukar samar da kudaden shiga ga kamfanoninsu, kasancewa kasar Sin tana matukar daukar hankalin 'yan kasuwa dake sha'awar sayen kayayyaki da masana'antun kasar Sin ke samarwa a farashi mai sauki.

Wanyoike ya ce, galibin 'yan kasuwar suna zuwa Guangzhou ne wanda daya daga cikin biranen kasuwancin kasar Sin dake kudancin kasar ta Sin.

Ya ce, Guangzhou ta kasance birni mafi shahara sakamakon masana'atun dake samar da kayayyaki masu inganci ga 'yan kasuwar kasar Kenyan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China