in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Sin ba za ta canja manufarta ta nuna sahihanci ga Afirka ba
2018-03-08 12:31:05 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, duk da sauyin yanayi da ake samu a duniya, maganganun da wasu suke fada, ba zai lalata zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ba, kuma kasar Sin ba za ta canja manufarta ta nuna sahihanci ga kasashen na Afirka ba.

Wang Yi ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru na zaman taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 wanda aka shirya a yau Alhamis a nan birnin Beijing. Wang Yi ya ce, kasashen Afirka na fuskantar manyan ayyuka biyu a yanzu haka, wato kiyaye zaman lafiya da tsaro, da kokarin farfadowa da samun ci gaba. Don haka, bisa hakikanan bukatun da kasashen Afirka suke da su ne, kasar Sin za ta kara shiga tsakani kan muhimman batutuwan nahiyar Afirka, da karfafa hadin kai tare da kasashe daban daban na nahiyar wajen yaki da ta'addanci da fashin jiragen ruwa, hana da kuma rigakafin hadari da dai sauransu, da nufin kara kwarewar kasashen Afirka na kiyaye zaman lafiya da tsaron su.

Baya ga haka, Wang Yi ya bayyana cewa, kasarsa na maraba da kasashen Afirka su ci gaba da samun moriya daga ci gaban kasar Sin.  Ya ce, a watan Satumban bana, za a shirya taron kolin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Afirka, mai taken raya "Ziri daya da hanya daya" tare, da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga bangarorin biyu. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China