Mr. Ikiara ya ce ko da yake da yawa daga masu zuba jari sun rika dari darin zuba kudaden su a cikin kasar, sakamakon dambarwar siyasar da aka fuskanta a bara, amma yanzu komai ya daidaita, kuma tuni an fara gudanar da hada hada bisa damar da kasar ke samarwa.
Jami'in wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce Kenya na da damammaki na zuba jari masu yawa, kuma gwamnati na da kyakkyawan fatan cin gajiya mai tarin yawa daga kudaden da za a zuba a matsayin jarin waje a cikin kasa.
Mr. Ikiara ya buga misali da kamfanin "Nippo Express" da babban ginin Pinnacle da aka kaddamar ba da dadewa ba, a matsayin alamu dake nuna fara hada hadar zuba jari a kasar. (Saminu)