in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta yi cikakken bayani game da 'yan mata 110 da suka bace
2018-02-28 09:11:42 cri
Hukumomi a Najeriya sun yi cikakken bayani game da 'yan mata 110 da aka sace a jahar Yobe dake arewa maso gabashin kasar.

A bakin ministan watsa labaran Najeriyar Lai Mohammed, wanda ya yi cikakken bayani kan lamarin a Abuja ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kafa wani kwamiti mai mutane 12, wanda zai gudanar da cikakken bincike kan musabbabin da ya haddasa sace 'yan matan makarantar sakadaren 'yan mata ta kimiyya da fasaha ta Dapchi a jahar Yobe, a ranar 19 ga watan Fabrairu.

An dai kammala tantance sunayen 'yan matan 110, gami da shekarunsu na haihuwa, da kuma ajujuwansu, in ji Lai Mohammed. Gwamnatin karamar hukumar Yobe ce ta samar da cikakkun bayanan 'yan matan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China