in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kaddamar da tsarin cinikin ikon fitar da iska mai kunshe da sinadarin Carbon
2017-12-20 13:13:53 cri

A ranar Talata gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wani tsarin cinikin ikon fitar da iska mai kunshe da sinadarin Carbon mai gurbata muhalli a duk fadin kasar, a matsayin wani matakin gwamnatin kasar na kafa kasuwar cinikin ikon iska mai kunshe da sinadarin Carbon mai gurbata muhalli wadda za ta kasance mafi girma a duniya.

A cewar kwamitin kula da ci gaba da sauye-sauye na kasar Sin wato NDRC wanda ke kula da harkokin raya tattalin arzikin kasar, da farko za a fara amfani da wannan tsarin ciniki ne a masana'antun samar da wutar lantarki.

Bisa wannan tsari, za'a tabbatar da masana'antun suna kiyaye adadin iska mai kunshe da sinadarin Carbon da aka ba su ikon fitarwa. Idan har ya kasance suna bukatar sama da abin da aka tanadar musu, to, wajibi ne su sayi adadin iska mai kunshe da sinadarin Carbon, daga masana'antun da ba su fitar da adadin iska mai kunshe da sinadarin Carbon da yawa ba su yi amfani da ita.

Da yake jawabi a taron manema labarai, Zhang Yong, mataimakin shugaban kwamitin NDRC ya ce, an zabi masana'antun samar da wutar lantarki ne domin fara amfani da wannan tsarin ciniki. Saboda a shirye suke wajen fara amfani da tsarin cinikin, kuma suna da cikakkun alkaluman adadin hayaki mai gurbata muhalli da suke fitarwa.

Zhang ya sheda wa manema labarai cewa, an shigar da kamfanonin samar da wutar lantarki sama da 1,700 a duk fadin kasar ta Sin cikin wannan tsarin ciniki, wadanda kuma baki daya suke fitar da hayaki mai gurbata muhalli fiye da ton biliyan 3. Don haka a mataki na farko kasuwar cinikin ikon fitar da iska mai kunshe da sinadarin Carbon ta kasar Sin za ta kasance kasuwa mafi girma a duk fadin duniya, ciki kuwa har da kasuwar kungiyar tarayyar Turai. (Ahmad&Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China