in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kara samun yawan adadin makamashin shale gas a 2016
2017-07-11 13:20:27 cri

Kasar Sin ta samar da karin nau'in gas da ake hakowa daga duwatsu wato shale gas a shekarar bara, a matsayinta na babbar kasa a duniya dake samar da makamashi da kuma amfani da makamashi mai tsabta domin maye gurbin yawan amfani da makamashin kwal da kasar tafi amfani da shi.

Adadin nau'in gas da ake hakowa daga duwatsu da kasar Sin ke samarwa ya karu da kashi 76.3 bisa 100 inda yawansa ya tasamma cubic mita biliyan 7.9 a shekarar 2016, wannan shi ne adadi mafi girma da kasar ta taba samarwa, kamar yadda ma'aikatar kula da kasa da albarkatun kasa (MLF) ta sanar a ranar Litinin.

Baki daya darajar kudinsu ya kai yuan biliyan 8.79 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.3, shi ne abin da aka kashe a fannin hako gas daga duwatsu a bara.

Kafa tarihin da kasar Sin ta yi a fannin kimiyyar hakar albarkatun kasa ne ya baiwa kasar damar zama a sahun gaba wajen samarwa duniya nau'in gas da ake hakowa daga duwatsu. Sai dai kasashe kadai ne a duniya suke iya samar da makamashin don sayar da shi a kasuwannin duniya, cikin kasashen har da Amurka, Canada da Argentina.

Gwamnatin kasar Sin tana yin wani shiri na kara yawan adadin albarkatun makamashin iskar gas da take amfani da shi da kashi 10 cikin 100 daga adadin kashi 5.9 cikin 100 nan da shekarar 2020, tana fatan kara yawansa zuwa kashi 15 cikin 100 nan da shekarar 2030.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China