A yau Laraba ne mista Wang Yi ya kawo karshen ziyarar ta sa a kasashen Rwanda, Angola, Gabon, gami da Sao Tome and Principe, hakan ya kasance karo na 28 a jere, da wani ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyarar farko a wata shekara ga nahiyar Afirka. Haka zalika ziyarar ita ce karo ta 13 da mista Wang Yi ya yi a nahiyar Afirka, bisa matsayinsa na manistan harkokin wajen kasar Sin.
A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ministan ya samu cimma ra'ayi daya tare da manyan jami'an kasashen 4, kan huldar dake tsakanin kasashensu da Sin, gami da manyan batutuwan kasa da kasa. Haka zalika, ministan kasar ta Sin ya bayyana wa jami'an kasashen 4 yanayin yadda taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya gudana, da shirin da aka tsara dangane da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, wanda zai gudana nan gaba cikin shekarar nan a birnin Beijing.
Ban da haka, ministan kasar Sin ya ce, kasarsa na son tsayawa kan manufofin tattaunawa tare da kasashen Afirka game da shirin da za a tsara, da gina wasu ayyuka tare da kasashen nahiyar, da raba moriyar da aka samu. Bisa wannan tushe ne, kasar za ta ci gaba da gudanar da ayyuka masu alaka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da kokarin samar da karin damammki ga hadin gwiwar da Sin da Afirka suke yi kan wasu manyan tsare-tsare.(Bello Wang)