Tuni ma bisa wannan tsari na hijira mai ruwa biyu, tare da aikin taimakawa 'yan gudun hijira da reshen HCR ya kaddamar, an kididdige 'yan gudun hijira fiye da dubu daya dake neman mafaka da suka fito daga kasashen Nijeriya, Afrika ta Tsakiya, Sudan da ma kuma 'yan kasashen Pakistan da Bangladesh dake isa birnin Agadez a cewar wasu majiyoyin na wannan hukumar kasa da kasa. Wakilinmu dake kasar Jamhuriyar Nijer Adam Maman ya aiko mana labarin. (Ada Maman)