Rahotanni daga Nijar din na cewa, rikicin ya barke ne, a lokacin da wasu manoman wurin suka yi korafin cewa makiyaya suna barin shanunsu su shiga gonakinsu, abun da ya sa manoman suka yi ramuwar gayya. Kawo yanzu rikicin ya hallaka a kalla mutane 34, kana, an kone gidaje sama da goma kurmus.
Rahotannin sun kara da cewa, an dade ana zaman doya da manja tsakanin manoma da makiyaya a yankunan kudancin Nijar, kana ana yawan samun hargitsi tsakaninsu sakamakon shiga gonakin manoma da dabbobin makiyaya suke yi.(Murtala Zhang)