in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko wadanne irin alfanun kasashen Afrika za su samu daga "taruka biyu" na kasar Sin
2017-03-17 12:55:55 cri

A watan Maris na kowace shekara kasar Sin ta kan gudanar da wasu muhimman taruka biyu, wadannan taruka su ne taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC a takaice, da kuma na majalisar bada shawara kan al'amurran siyasa ta kasar Sin CPPCC. Tarukan biyu sun kasance muhimman tarukan siyasar kasar Sin dake jan hankalin kasashen duniya baki daya, inda a lokacin tarukan ne ake nazartar batutuwa da dama da suka shafi makomar kasar ta fuskar tsara fasalin tattalin arziki, siyasa, raya al'adu, kyautata zaman rayuwar al'ummar Sinawa, da batun huldar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen duniya da dai sauran batutuwa.

To ko wadanne irin alfanun kasashen Afrika za su samu daga cikin wadannan tarukan biyu, jakadan Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya yi dogon sharhi kan wannan batu:

Tarukan biyu na wannan shekara sun kasance na farko da kasar Sin ta gudanar a farkon wannan shekara a matsayin muhimman tarukan siyasar kasar tun bayan taron siyasar da aka gudanar a watan Oktoban bara, a zama na 6 na taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 CPC, inda aka tabbatar da matsayin babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping na kasancewar babban shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A wajen babban taron CPC karo na 19 wanda ake saran gudanar da shi tsakanin watan Yuli zuwa na Disamban wannan shekarar, za'a gudanar da zaben sabbin shugabannin da zasu ja ragamar jam'iyyar ta CPC, kana taron zai tsara jadawalin da zai tabbatar da makomar tsarin siyasar kasar a nan gaba. Wadannan taruka biyu sun kasance a matsayin mabudi game da share fagen gudanar da zaben jam'iyyar. Bugu da kari, kasar Sin ta cimma nasarori masu yawa a shekarar data gabata musamman wajen aiwatar da shirin nan na shekaru biyar biyar karo na 13 wanda ya kunshi shirin bunkasa cigaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma wato daga shekarar 2016-2020. Wannan shiri ya haskakawa duniya game da irin tasirin da wadannan tarukan biyu ke yi wajen kyautata rayuwar al'ummar Sinawa da cigaban tattalin arzikin kasar.

Kasashen Afrka sun kasance manyan aminai ga kasar Sin ta fuskar huldar diplomasiyya da harkokin ciniki da dai sauransu. To ko wane alfanu kasashen nahiyar Afrika zasu samu daga wadannan tarukan biyu? Da farko dai akwai kyakkyawan fata da duniya ke da shi game da kyautatuwar yanayi da tattalin arzikin Sin ya samu. A shekarar 2016 data gabata, kasar Sin ta samu bukasuwar tattalin arziki da kashi 6.7% na GDP, adadin da ya dara hasashen karuwar tattalin arikin da duniya tayi game da Sin, adadin ya zarta na kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki. Wasu alkaluman kididdiga da asasun bada lamini da kasa da kasa wato IMF yayi ya nuna cewa, a shekarar data gabata, kasar Sin ta tallafawa cigaban tattalin arzikin duniya da kashi 39 cikin 100. Karuwar tattalin arzikin na Sin ya samar da yakini, kana ya zama babban jigon samun daidaito da kuma bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. Kasar Sin ta samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 13 a yankunan birane, kana ta tsame al'ummar dake zaune a karkara sama da mutane miliyan 12 daga kangin talauci, sannan ta janyo hankalin jarin kai tsaye na kasashen waje FDI da ya zarta dalar Amurka biliyan $130 a shekarara 2016.

A yanzu haka, kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma kasa ta biyu mafi samar da jarin kai tsaye na kasashen waje a duniya, kasa mafi samar da kayayyaki a duniya, kasar mafi samar da kasuwa a fannin yawon bude ido, kana kasa mafi girma wajen huldar cinikayya da kasashen duniya wacce a halin yanzu take mu'amalar kasuwanci da kasashen duniya sama da 120.

Kasar Sin ta aza kyakkyawan tubalin samun bunkasuwar tattalin arziki, kuma tattalin arzikinta yana cigaba da samun tagomashi da kuma kyakkyawan yakini.

Abu na biyu, kasahen Afrika suna da manya manya damammaki daga kasar Sin. Firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada muhimmanci wannan batu cikin rahotonsa game da ayyukan gwamnati a ranar 5 ga watan Maris, ya ce "kasar Sin tana adawa da duk wani batu na yin baba-kere a dukkan fannoni, kuma tana da tsari game da fasalin tattalin arzikin duniya wanda zai ba da damar cin moriya a tsakaninn dukkan bangarori, da nuna adalci da daidaito. Kasar Sin zata daga matsayin huldarta da kasashe masu tasowa, kana zata samar da wani shiri wanda ya shafi warware takaddamar kasa da kasa da na shiyya".

A shekarar 2016 kadai, kasar Sin ta samar da dala biliyan $170 ga fannin zuba jarin kasashen ketare, kuma al'ummar Sinawa miliyan 120 sun ziyarci kasashen duniya dabam dabam don yawon bude ido. Nahiyar Afrika ta kasance muhimmin waje da Sinawa ke sha'awar ziyarta domin yawon bude ido.

Wannan babbar dama ce ga Sin da Afrika wajen yin cudanya da juna domin samun cigaba tare da kuma tabbatar da mafarkin da Afrika ta jima tana yi na samun bunkasar masana'antu.

Abu na uku, Sin da Afrika zasu kara kaimi wajen aiwatar da shirin nan na dangantar Sin da Afrika wato FOCAC wanda aka kaddar a Johannesburg a shekarar 2015, inda kasar Sin ta ware dala biliyan $60 don aiwatar da shirin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China