in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron shekara shekara na majalisar CPPCC
2018-03-03 17:53:34 criYau Asabar da yamma, a birnin Beijing, aka kaddamar da zaman taron farko na kwamitin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 13. Shugaban majalisar, Mista Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoton aiki, inda ya ce, ya kamata majalisar CPPCC ta yi kokarin koyon tunanin babban taron wakilai karo na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda aka yi a bara, kana, ya kamata 'yan majalisar CPPCC su sauke nauyin dake kansu, ciki har da bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, da sa ido kan harkokin kasa bisa tafarkin demokuradiyya, da kuma shiga cikin harkokin siyasa na kasa, ta yadda za su bayar da sabuwar gudummawa ga raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi, da kuma raya kasar Sin mai tsarin gurguzu kuma mai zamani.

Da misalin karfe uku na yammacin yau Asabar, aka bude zama na farko na majalisar CPPCC a karo na 13 a birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping da dai sauran wasu shugabannin kasar suka hallara.

Shugaban majalisar CPPCC karo na 12 Mista Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoton aiki, inda ya nuna cewa, a cikin shekaru biyar da suka shige, majalisar CPPCC ta maida hankali sosai kan muhimman ayyuka na jam'iyyar kwaminis gami da na kasar Sin baki daya, da gudanar da ayyukanta domin kawowa al'umma moriya da alheri. Ya na mai cewa:"Majalisar CPPCC ta maida hankali kan wasu batutuwan da suka jibinci zaman rayuwar al'umma, da kuma zurfafa shawarwari a kansu, ciki har da sa ido kan ingancin abinci, da daidaita tsarin gidaje, da samar da guraban ayyukan yi ga jama'a, musamman ma daliban jami'o'in da suka gama karatu gami da sojojin da suka yi ritaya, da kulawa da tsoffi, tare kuma da kare hakkin wasu gungun mutane na musamman, kamar ma'aikatan tsabatace tituna, da manoma 'yan ci rani, da masu bukata ta musammam, da sauransu."

Majalisar CPPCC, hukuma ce dake karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda ke hada kan jam'iyyu daban-daban da bada shawarwari kan harkokin siyasa.

Da ya waiwayi ayyukan da majalisar ta gudanar cikin shekaru biyar da suka gabata, Mr.Yu Zhengsheng ya yi nuni da cewa, babbar manufar siyasa da ta zama wajibi ga majalisar ita ce gudanar da harkoki daban daban karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar, sa'an nan a tsaya kan matsayin majalisar na dandalin yayata dimokuradiyya da kuma tsoma baki cikin harkokin kasa da ma karfafa hadin kai a tsakanin jam'iyyun siyasa da kuma sassa daban daban, inda ya ce, "Ya kamata a tsaya kan neman cimma daidaito baki daya ta hanyar yin shawarwari da yayata manufar dimokuradiyya da kuma manufar yin shawarwari, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau da 'yan majalisar suke son ba da shawarwarinsu da kuma fadin gaskiya. Muna son a rika shawarwari da juna ba tare da gaba ba, sannan a yi sahihan shawarwari, tare da kokarin kara cimma daidaito da juna da karfafa hadin kai."

A bana ne ake cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, haka kuma wata muhimmiyar shekara ce ta fannin cimma burin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi. A cewar Mr.Yu Zhengsheng, majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin za ta yi kokarin sauke nauyin da ke wuyanta na bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar, da sa ido kan harkokin kasa bisa tafarkin demokuradiyya, da kuma shiga cikin harkokin siyasar kasa, don ba da gudummawarta wajen raya kasar Sin mai tsarin gurguzu na zamani

Bisa ajandar babban taron, yayin zaman taron farko na CPPCC karo na 13, za a dudduba rahoton ayyukan zaunannen kwamitin majalisar karo na 12, da rahoton shawarwarin da majalsar ta gabatar, da tsarin dokokin majalisar da aka yi wa gyara. Baya ga haka, za a zabi sabbin shugabannin majalisar, da kuma halartar zaman taron farko na majalisar NPC bisa matsayinsu na 'yan kallo.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China