Kasar Sin za ta ciyar da aikin gina shirin ziri daya da hanya daya gaba, inda za ta kafa yankunan gwajin ciniki cikin 'yanci a birnin Shanghai da sauran wurare 11, da kuma yankunan cinikin yanar gizo 13, tsakaninta da kasashen ketare.
Haka kuma, adadin kwararru 'yan ketare da za su zo aiki a kasar Sin, zai karu da kashi 40 bisa dari. Har ila yau, za a kulla tare da kyautata yarjejeniyoyin ciniki cikin 'yanci guda 8. Kana, za a shigar da kudin Sin wato RMB cikin kwandon kudaden musamman na Asusun ba da lamuni na IMF. (Maryam Yang)