Wannan "wani sabon tsarin jam'iyyu ne dake samun tagomashi wanda kasar Sin ta bullo da shi", in ji shugaba Xi, kana babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin tsakiya na dakarun tsaron kasar Sin, ya furta hakan ne a lokacin da ya halarci taron tattaunawa da jiga-jigan siyasa da suka fito daga gamayyar jam'iyyun kasar Sin wato China Democratic League da kuma jam'iyyar China Zhi Gong Party, wannan ya kunshi mutanen da ba su da alaka da wata jam'iyyar siyasa da kuma Sinawana da suka dawo daga kasashen ketare, inda suka gana a zaman farko karo na 13 na taron kwamitin ba da shawara kan al'amurran siyasar kasar Sin (CPPCC).
Ya ce a halin yanzu, an jingine tsoron tsarin siyasa da ake amfani da shi mai cike da rauni, wanda wasu jam'iyyun siyasa, da wasu shafaffu da mai, da kungiyoyin addinai, suke raba kan al'umma.
Xi ya ce, bin tsarin shugabancin jam'iyyar CPC ba ya nufin yin watsi da tsarin demokaradiyya ba ne.
A maimakon hakan, JKS na kokarin kafa wani tsarin demokaradiyya mai fadi kuma mai matukar inganci. (Ahmad Fagam)