#taruka2na2018# Kasar Sin ta ba da gudummawar da ta zarce kashi 30% ga ci gaban tattalin arzikin duniya
Gwamnatin kasar Sin a yau Litinin ta gabatar da wani rahoto ga hukumar kolin kasar, inda ta yi nuni da cewa, cikin shekaru biyar da suka wuce, jimillar alkaluman tattalin arziki wato GDP na kasar, ta karu daga kudin kasar yuan biliyan dubu 54 zuwa biliyan dubu 82.7, abun da ke nufin tana karuwa da kashi 7.1% cikin kowace shekara. Sa'an nan kason da tattalin arzikin kasar ke dauka cikin gaba dayan tattalin arzikin duniya ya karu daga kashi 11.4% zuwa kimanin kashi 15%, kuma yawan gudummawar da kasar ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ya zarce kashi 30%. Har wa yau, gwamnatin kasar ta kayyade gibin kudin kasar da ya kai kasa da kashi 3%.(Lubabatu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku