#taruka2na2018# Yawan karuwar GDP na kasar Sin a bana zai kai kashi 6.5 bisa dari
Bisa rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar ga cikakken zama farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, an yi hasashen cewa, a shekarar da muke ciki, karuwar alkaluman GDP na kasar Sin zai kai kashi 6.5 bisa dari, kana, alkaluman farashin kayayyakin masarufi wato CPI, zai karu da kashi uku bisa dari. Har wa yau, za'a kara samar da guraban ayyukan yi ga mutane sama da miliyan 11 a birane da garuruwan kasar a bana. (Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku