Jami'in ya ce, cikin shekarun da suka gabata, kasar Sin ta kara ware kudi a fannin tsaro, musamman domin cike gibin da aka fuskanta a baya da ma gyara damarar soja, da kuma kyautata rayuwar sojoji. Ya jaddada cewa, yawan kudin da kasar Sin ta ware a fannin tsaron kasar bai kai matsayin manyan kasashen duniya ba, idan aka yi la'akari da yawan GDP na kasar da kason da aka kebewa tsaro a kasafin kudin kasar baki daya, ko kuma idan aka kwatanta da yawan kudin tsaro da aka ware da yawan al'ummar kasar.
Ya nanata cewa, kasar Sin tana nacewa ga bin hanyar lumana da kuma manufar tsaron kanta, kuma ci gaban kasar ba zai haifar da barazana ga kowace kasa ba.(Lubabatu)