Mai magana da yawun babban taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar Sin ya kasance wani muhimmin aiki da taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13 zai mayar da hankali kansa.
"Kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya bayyana niyyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ta al'ummar sinawa, ya kasance muhimmin ginshiki na dokokin kasar Sin, kana shi ne muhimmin ginshikin tafiyar da sha'anin mulkin kasar Sin da tabbatar da tsaron kasar", in ji Zhang Yesui, kakakin taron NPC karo na 13, wanda ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a birnin Beijing.
Zhang ya ce, an yi amana cewa kundin tsarin mulkin da kasar Sin ke amfani da shi a halin yanzu shi ne mafi dacewa da yanayin kasar ta Sin, kuma yana biyan muradun kasar da al'ummarta a wannan zamanin da muke ciki.
Ya ce, ya zama tilas a yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin ya kunshi muhimman manufofin JKS, da muradun al'ummar Sinawa, da manyan nasarorin da kasar ta samu, ta yadda za a tabbatar da ganin kundin tsarin mulkin kasar ya taka muhimmiyar rawar da ake fata wajen daga martabar kasar da kuma cigaban tsarin gurguzu wanda ya dace da halayyar musamman ta kasar Sin a sabon karni.(Ahmad Fagam)