in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar ziri daya da hanya daya ba wai manufar cimma moriyar kasar Sin ba ne
2018-03-04 14:26:19 cri
A bana ake cika shekaru biyar da kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya. Kakakin taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Yesui a yau Lahadi ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, furucin nan na wai manufar ziri daya da hanya daya manufa ce ta cimma moriyar kasar Sin tamkar gurguwar fahimta ne a kan manufar shawarar.

Mr. Zhang Yesui ya yi nuni da cewa, shawarar ziri daya da hanya daya shawarar hadin gwiwar tattalin arziki ce dake da burin samun moriyar juna, wadda take neman samar da damar bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma ci gaban kasa da kasa baki daya. Shawarar a bude take ga ko wace kasa dake da sha'awar shiga a dama da ita.

Kakakin ya kara da cewa, cikin shekaru biyar da suka gabata, a kokarin da kasa da kasa suka yi tare, an cimma manyan nasarori wajen aiwatar da shawara ziri daya da hanya daya, musamman ta fannonin raya manyan ayyuka da zirga-zirga da tuntubar juna kan manufofi da inganta tsarin hadin gwiwa da juna, ana kuma aiwatar da hadin gwiwa ta fannoni daban daban.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China