Yau Lahadi, mai magana da yawun babban taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ba za ta kwafi salon wata kasa a duniya ba, kana ba za ta tilastawa wata kasa yin amfani da irin salon da take amfani da shi wajen cigaban kasarta ba.
Zhang Yesui, kakakin babban taron wakilan jama'ar Sin NPC karo na 13, ya fada a lokacin taron manema labarai cewa, kasar Sin za ta cigaba da bin salo mai sigar da ta dace da tsarin kasarta, kuma ba za ta umarci wata kasa a duniya ta yi koyi da irin salon kasar ta Sin ba.
Zhang ya ce, ba zai taba yiwuwa tsarin cigaban wani ya dace da na kowa da kowa ba, kuma ko wace kasa tana bin tsarin da ya yi daidai da yanayin bukatun kasarta ne.
Kasar Sin ba za ta taba neman maye gurbin salon da kasa da kasa ke amfani da shi a halin yanzu ba, za ta ci gaba da kare manufofi da kuma bada gudunmowa ga tsarin kasa da kasa, in ji Zhang.
Ya ce kasar Sin a shirye take ta shiga a dama da ita a tsarin gudanarwar kasa da kasa, da kawo sauyi mai ma'ana, da gina cigaba, da kuma tabbatar da bunkasuwar harkokin kasa da kasa domin tabbatar da adalci da samun daidaito.(Ahmad Fagam)