in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta rantsar da jami'an sassan gwamnati bisa tanadin kundin tsarin mulki bayan zabensu
2018-03-04 18:26:23 cri
A gobe Litinin ne za a kaddamar da zaman taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a nan birnin Beijing. A yayin taron manema labarai da aka kira a yau Lahadi, kakakin taron Mr. Zhang Yesui ya bayyana cewa, za a gudanar da bikin rantsar da jami'an sassan gwamnatin ne bisa dokar kundin tsarin mulkin kasar bayan da aka zabe su da tabbatar da nada su.

Kakakin ya jaddada cewa, bikin zai kasance irinsa na farko da za'a gudanar a gun taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tun bayan da aka fara aiwatar da manufar rantsar da jami'an gwamnati bisa tanadin dokar kundin tsarin mulkin kasar, matakin kuma da zai iya kara kiyaye kwarjinin tsarin mulkin kasar ta Sin da kuma yayata shi.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China