A gun taron manema labaru da aka gudanar game da taron a yau Lahadi, sabon kakakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a wannan karo Zhang Yesui ya bayyana cewa, akwai ayyuka 10 da za a gudanar a taron a wannan karo, ciki har da sauraron rahoton ayyukan gwamnatin kasar, da duba rahoto game da yadda ake aiwatar da shirye-shiryen kasar, da shirin kasafin kudin kasar, da duba daftarin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, da dokokin sa ido kan harkokin kasar, da rahoton ayyukan zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar, da rahoton ayyukan kotun koli ta kasar, da hukumar koli gabatar da kararraki ta kasar, da shirin yin kwaskwarima kan hukumomin majalisar gudanarwar kasar, da zaben jami'an hukumomin gwamnatin kasar da dai sauransu.
An ce, za a kira tarurukan manema labaru 14 a yayin taron, tarukan da za su shafi manyan batutuwan da ke jawo hankalin al'umma, ciki har da gyara kundin tsarin mulki da kafa dokoki, da harkokin sa ido. A safiyar ranar 20 ga wannan wata ake saran rufe taron, sabon firaministan kasar zai gana da 'yan jarida na gida da na waje tare da amsa tambayoyinsu. (Zainab)