Wajen taron, Wang ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin tabbatar da samun kwanciyar hankali a duniya, da ciyar da tattalin arzikin duniya gaba, tare da samar da gudunmowa ga daidaita tsarin kula da duniyarmu.
Lokacin da ya ambaci huldar dake tsakanin Sin da Afirka, ministan kasar Sin ya ce Sin tana kokarin cika alkawarin da ta yi, kan tallafawa kasashen Afirka. A cewarsa, ana sauya tsarin hadin gwiwar Sin da Afirka bisa bukatun kasashen Afira. Wato na farko, gwamnati tana sakarwa kasuwanni iko na kula da hadin gwiwar. Na biyu ya ce ko da yake tun a baya ana mai da hankali kan cinikayya, amma yanzu an fi dora muhimmanci kan raya masana'antu a Afirka. Sa'an nan na 3, a baya ana karbar kwangilar gini kawai, amma yanzu bayan kammala aikin gini, bangaren Sin na kara zuba jari don kula da ayyukan da aka aiwatar.
Dangane da huldar dake tsakanin Sin da Amurka, minista Wang ya ce, kasar Sin da kasar Amurka suna musayar ra'ayi don karfafa mu'amala tsakanin shugabannin kasashen 2, gami da kara yin hadin gwiwa a sauran fannoni.(Bello Wang)