Taron dai zai tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasar, da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar, da kuma cimma matsaya game da takamammen lokacin da za'a gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa.
Da ma dai shugaba Buhari ya nada Bola Tinubu, tsohon gwamnan jahar Legas, domin ya jagoranci kwamitin tuntuba da sasanta rikice-rikicen da ya addabi jam'iyyar ta APC mai mulkin kasar.
Ayyukan da aka damkawa Tinubu, sun hada da warware rashin fahimtar juna da takun-saka a tsakanin mambobin jam'iyyar, da masu rike da mukaman siyasa a wasu jihohin kasar.
Shi dai babban taron jam'iyya, ya kasance a matsayin wani dandali ne dake baiwa jam'iyya damar yin gyare gyare kan manufofinta da tsare-tsarenta, da kuma zabar jagorori da yin sauye-sauye a tsarin shugabancin jam'iyyar da yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin jam'iyyar da dai sauransu.
A watan Fabrairun shekarar 2019 ne za'a gudanar da manyan zabuka a Najeriya. (Ahmad Fagam)