Babban sakataren jam'iyya mai mulkin Kenya wato jam'iyyar Jubilee, Raphael Tuju ya jaddada cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ya shaida cewa, kar a kwaikwayi tsarin siyasa da tsarin demokuradiyya irin na kasashen yammacin duniya daga dukkan fannoni. Kenya na bukatar koyon nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta samu, a fannonin da suka shafi alaka tsakanin kabilu da raya kasa da jam'iyyun siyasa da kuma lalibo wata hanyar da ta fi dacewa wajen neman bunkasa.
Shi ma a nasa bangaren, shehun malami Otiato Wafula daga sashin nazarin ilimin siyasa na jami'ar Kenyatta dake kasar Kenya ya ce duk da cewa yanayin da ake ciki a kasar Sin da na Afirka ba daya ba ne, amma suna da muhimman ayyuka kusan irin daya, wadanda suka hada da habaka tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma da kuma kawar da talauci. Malamin ya ce, tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya samar da wata muhimmiyar turba da jama'ar kasar za su bi don neman ci gaba a fadin kasar.(Murtala Zhang)