Ofishin zaunannen kwamitin majalisar NPC, gami da na majalisar CPPCC na maraba da 'yan jaridu na gida da waje, da su bada rahotanni game da tarukan biyu.
Ana bukatar 'yan jaridu da su gabatar da takardar neman samun izini don bada rahotannin. Haka kuma, 'yan jaridun kasashen waje dake aiki a kasar Sin, ya kamata su mika takardar neman izini ga cibiyar watsa labarai ta tarukan biyu, yayin da su kuma 'yan jaridun da za su zo nan kasar Sin takanas don tarukan biyu, ake bukatar su da su gabatar da takardar neman izini ga cibiyoyin bada takardun biza na ofisoshin jakadancin Sin dake kasashensu, ko sauran wasu cibiyoyin bada biza da ma'aikatar harkokin wajen Sin ta amince da su.
An kuma tsara cewa, 'yan jaridun za su gabatar da takardun neman iznin kafin ranar 25 ga watan nan da muke ciki. (Murtala Zhang)