Yau Jumma'a a birnin Beijing, aka shirya taron manema labarai game da zaman taron farko na majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 13. Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki a halin yanzu, mai magana da yawun zaman taron, Mista Wang Guoqing ya bayyana cewa, habaka tattalin arzikin kasar ta hanyar da ta dace, shi ne muhimmin aikin da za'a sanya gaba.
Mista Wang ya ce, tattailn arzikin kasar Sin ya shiga cikin wani sabon yanayi, kuma kamata ya yi a kara maida hankali kan raya tattalin arziki mai inganci, da sauya hanyoyin da ake bi wajen habaka shi.(Murtala Zhang)