A farkon watan nan ne kasar Sin ke shiga lokacin gudanar da tarukan siyasarta na shekara-shekara. Yayin da majalisar wakilan jama'ar kasar da majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar ke shirin gudanar da tarukansu na shekara domin tsara manufofin kasar na bana da shekaru masu zuwa, manazarta na sa ran manufar ta 'samar da kyakkyawar makomar' ita ce za ta zama jigon taron na bana.
Manazartan na ganin za a iya gabatar da kudurin sanya manufar cikin kundin tsarin mulkin kasar yayin tarukan. (Fa'iza Mustapha)