in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bayyana kwarin gwiwa wajen ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su
2018-02-27 09:21:40 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fada a jiya Litinin cewa, dukkan mutanen da kungiyoyin ta da kayar baya suka yi garkuwa da su, ciki har da 'yan matan makarantar sakandaren kimiyya da fasaha ta Dapchi dake jahar Yobe, za'a ceto su lami lafiya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja, babban birnin kasar, a lokacin da ya karbi bakuncin malaman jami'ar Maiduguri su 3 da matan jami'an 'yan sandan kasar 10 a fadar shugaban kasar, wadanda aka kubutar daga hannun mayakan 'yan ta'adda.

Ya shedawa mutanen cewa, tun tuni ya baiwa dukkan hukumomin tsaron kasar umarnin su tabbatar da kubutar da 'yan matan makarantar da aka yi garkuwa da su a shiyyar arewa maso gabashin kasar da sauran sassan kasar baki daya.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.

Shugaban kasar ya shedawa mutanen da aka kubutar cewa, ban da iyalansu, dukkan wani dan Najeriya mai kaunar zaman lafiyar kasar ya yi ta addu'a da nuna fatar ganin an kubutar da su daga hannun mutanen da suka yi garkuwa da su.

Shugaban Najeriyar ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya tana yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin ganin an inganta yanayi da kuma sake tsugunar da mutanen da rikicin 'yan tada kayar baya ya raba su da gidajensu.

Mutanen da aka ceto suna karkashin kulawar jami'an tsaron farin kaya a Abuja, inda tawagar likitoci da masana halayyar dan adam ke ba su kulawa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China