in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Iraki ta yi kira ga gwamntin kasar da ta tsara ajandar janye sojojin kasashen ketare daga kasar
2018-03-02 11:01:31 cri

Majalisar dokokin Iraki, ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta tsara ajandar janyewar sojojin kasashen ketare daga kasar.

Wata sanarwa da Majalisar ta fitar a jiya, ta ce 'yan majalisar sun zartas da wani kuduri ta hanyar kada kuri'a, inda suka bayyana godiya ga dukkanin kasashen da suka goyi bayan Iraki wajen yaki da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS, tare kuma da yin kira ga gwamnatin kasar da ta tsara ajandar da aka ambata a baya, bayan an samu nasarar yaki da kungiyar IS.

Bisa tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar da kasashen Amurka da Iraki suka daddale a shekarar 2008 dangane da matsayin sojojin Amurka, an shirya kammala janye sojojin Amurka daga Iraki kafin karshen shekarar 2011, tare da jibge wasu a cikin ofishin jakadancin Amurka da ke Irakin. Sai dai a shekarar 2014 ne kuma, kungiyar IS ta mamaye yammacin Iraki da yawancin arewacin kasar, inda Amurka ta kara tura sojojinta kasar.

A ranar 9 ga watan Disamban bara ne firaministan Iraki Haider al-Abadi ya sanar da cewa, sojojin gwamnatin kasar sun kwace dukkanin yankunan da kungiyar IS ta taba mamayewa, ya na mai cewa Iraki ta samu gaggarumar nasarar a yakinta da kungiyar IS.

A farkon watan Febrairun da ya gabata ne kuma, Iraki ta ce ta daddale yarjejeniya da Amurka, dangane da rage yawan sojojinta dake kasar sannu a hankali. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China