in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi tir da harin kunar bakin wake a Bagadaza
2018-01-16 13:32:17 cri

Jiya Litinin 15 ga wata, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya fidda wata sanarwa ta hannun kakakinsa, wadda da babbar murya ya yi tir da harin kunar bakin wake da aka kaddamar a birnin Bagadaza, fadar mulkin kasar Iraki.

Cikin sanarwarsa, babban magatakardar MDDr ya sake nanata cewa, MDD za ta ci gaba da mara wa gwamnatin kasar Iraki da jama'ar kasar baya wajen yaki da 'yan ta'adda, da kuma farfado da kasar ta Iraki.

A ranar Litinin din ne dai aka kaddamar da hare-haren kunar bakin wake guda 2, a filin al-Tayaran mai cunkuson mutane, wanda ke cibiyar birnin Bagadaza. Maharan 2 sun tayar da boma-bomai da suka boye a jikinsu, a dab da wasu masu aikin gine-gine, harin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 27, yayin da wasu 91 suka jikkata.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta yi shelar daukar alhakin kaddamar da hare-haren. Ko da yake a baya, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS ta sha kaddamar da makamantan wadannan hare-hare a kasar ta Iraki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China