in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Iraki ya amince da a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar a watan Mayu
2018-01-23 11:19:24 cri
Jiya Litinin, shugaban kasar Iraki, Fouad Masoum, ya amince da a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar a sabon karo a ranar 12 ga watan Mayun bana.

Tun a wannan rana, majalisar dokokin Iraki ta zartas da wani kuduri, inda aka tabbatar da cewa, za'a gudanar da zaben ne a ranar 12 ga watan Mayun bana.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar, tsawon wa'adin aiki na 'yan majalisar dokoki a kowane karo ya kai shekaru hudu. Gwamnatin Iraki gami da kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar su ne za su tabbatar da lokacin gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, kana, idan majalisar dokokin kasar ta amince da lokacin, za'a mika shi zuwa ga shugaban kasa don ya amince da shi.

An yi irin wannan zabe ne a kasar Iraki a ranar 30 ga watan Afrilun shekara ta 2014.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China