in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Iraki na ci gaba da kai samame kan IS
2017-12-17 13:15:51 cri
Jiya Asabar, sojojin kasar Iraki sun fara daukar matakin soja a kauyukan dake tsakiyar kasar, don kai samame kan maboyar 'yan kugiyar IS mai tsattsauran ra'ayi.

Sanarwar da ofishin jagorantar matakan soja na hadin gwiwa na kasar Iraki ya bayar ta nuna cewa, a wannan rana, sojojin sun fara daukar matakin soja a iyakar dake tsakanin lardunan Salahudin da Diyala, inda suka ragargaza wani wurin da 'yan kungiyar IS ke boye.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, sojojin gwamnatin Iraki sun kame sansanonin IS dake lardunan Salahudin da Kirkuk, hakan tasa wasu dakarun sun tsere zuwa yankin Mteibijah.

A ranar 9 ga wata, firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya sanar da cewa, sojojin gwamnatin sun riga sun kame duk yankunan da 'yan kungiyar IS suka mamaye, kasarsa ta samu cikakkiyar nasara wajen murkushe kungiyar. Amma har zuwa yanzu, akwai wasu 'yan kungiyar da suke boye a hamada da duwatsu dake kasar, don kokarin samun damar kai farmaki. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China