in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraqi sun kashe mayakan IS 15 a kusa da iyakar kasar da Syria
2018-01-03 10:44:21 cri

Ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Iraqi, ta ce dakarun Gwamnati sun kashe mayakan IS 15 dake kokarin shiga kasar daga Syria.

Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Brig.Janar Saad Maan ya fitar , ya ce bisa rahotannin sirri da aka samu, jami'an 'yan sanda da na hukumar leken asiri, sun yi wa mayakan IS 15 kwantan bauna tare da halaka su a lokacin da suke kokarin shiga Iraqi ta kan iyakarta da Syria a yankin yammacin kasar.

Saad Maan ya ce hukumar leken asirin ta gano 'yan ta'addan masu dauke da makamai da ababen fashewa da suka daura a jikinsu, inda ta yi ta bibiyarsu tsawon kwanaki kafin a halaka su.

A ranar 9 ga watan Disamban da ya gabata ne, Firaministan Iraqi Haider al-Abadi, ya sanar da fatattakar mayakan IS daga kasar, bayan jami'an tsaro sun kwace iko da dukannin yankunan dake kan iyakarta da Syria da na sahara dake yammacin kasar daga hannun kungiyar.

Sai dai har yanzu daidaikun mayakan na kokarin shiga Iraqin daga makociyarta Syria ta iyakar dake da nisan kilomita 600 mai tsaunuka da kuma yankin sahara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China