Asusun tallafawa kanana yara na MDD (UNICEF) a takaice ya sanar da cewa, tun bayan da aka kaddamar da yaki kan mayakan IS a kasar Syria, yaro daya cikin yara hudu a kasar Iraki yana fama da talauci.
Wata sanarwa da asusun na UNICEF ya fitar a jiya Lahadi ya bayyana cewa, duk da cewa, an samu kwanciyar hankali a kasar ta Iraki, amma tasirin rikicin ya shafi miliyoyin mutane a sassan kasar daban-daban, inda daya cikin hudu na yaran kasar ke rayuwa cikin kangin talauci, lamarin da ya cusa iyalai daukar wasu matakai masu tsauri domin su rayu.
A don haka, asusun ya bukaci kasashen duniya da su ba da gudummawa wajen sake gina muhimman kayayyakin more rayuwa da kuma taimakawa yaran dake cikin mawuyacin hali a kasar ta Iraki.
Sanarwar asusun na zuwa ne kwana guda kafin taron kasashe da kungiyoyin dake ba da gudummawa na kasa da kasa da za a kira a Kuwait daga yau Litinin zuwa ranar 14 ga wata, inda ake sa ran za a sanar da gudummawar kudaden sake gina kasar ta Iraki.(Ibrahim)